Uzairu badamasi

BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA

Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!


Shafin farko

Haidar Ali

Tambayoyi da amsarsu tare da
Mallam Ibrahim Zakzaky na goma sha takwas


Sayyed Zakzaky2

Ko ya halatta Likita ya bada maganin zubar da ciki?
TAMBAYA: Akramakallah, ko ya halasta ga likita ko mai ba da magani ya bayar da maganin da zai zubar da ciki ga matar da ta zo tare da mijinta saboda tana shayar da wani yaron?

Daga Alhaji Shehu Usman Mairuwa Funtuwa

SHAIKH ZAKZKY: Idan dai ciki din ya kai wani mikdari wanda ana iya cewa an sami kamalan da a ciki, to zai zama ma kisan kai ne, sai dai hukuncinsa ba irin na a kashe mutum bane. Zai zama akwai diyyar tayi, wanda shi ne za a biya. Amma idan bai kai nan ba, sai a ce sun aikata haramun. Ba inda aka ce miji da mata sun samu su zubar da ciki, lallai ba su sami haka nan ba. Ta hanya guda ce zubar da ciki zai iya halasta, shi ne inda binciken Likita ya nuna cewa imma dai ta haihu ta mutu ko kuma a zubar da ciki din, to wannan ne kawai. Don a ceci nata ran, sai zabi tsakanin abin da yake cikin cikinta don a ceci ranta, wato a fifita rayuwarta a kan abin da yake cikinta. Amma in ba ta wannan fuska ba, ba ta inda zubar da cikin yake halatta.


TAMBAYA: Allah shi gafarta Malam, mutum ne yake bin mazhabar Maliki, sai ya ga wani hukunci a wata mazhabar, shin ya halasta ya dauka ko a'a?

Daga Shafi'i Abubakar Wababi

SHAIKH ZAKZAKY: To wannan in ya tambayi Mazhabar Malikiyya zai ji bayani sosai. Duk ma'abota Mazhabobin nan na Ahlus sunnati ba wanda ya ce shi Mazhabarsa ita ce kawai addini, an gama. Har ma akwai wadanda suke cewa in an ga wani abu wanda ya fi nasu, to a koma ga wancan. Kuma cikin masu fadin wannan har da shi Imam Malik, Limamin Mazhabar Malikiyya din. Kuma kamar fadin Shehu Usman Danfodiyo da yake cewa, Ka sani ya dan uwa Allah bai lizimta mana wata mazhaba, ya ce ga mazhaba wance za ku bi ba. Mazhaba tamkar ra'ayi ne na wannan Malamin, abin da ya tafi a kai. Saboda haka yana da madogara, imma dai fahimtarsa ko kuma ya dogara da hadisi. Saboda haka ba a kayyade ka da bin mazhabar Malikiyya lazim ba, ko da ka ga wani abu a wani wuri, wanda yake ya fi na Malikiyya; wajibinka ne ma ka koma ga abin da ya fi na Malikiyya in ka gani.

TAMBAYA: Allah shi gafarta Malam, shin da gaske ne zakka ba ta hau kan takardar kudi ba?

Daga Shafi'u Abubakar Wababi

SHAIKH ZAKZAKY: Akwai abubuwan da aka ambata wadanda zakka take hawa kansu, ciki har da zinare da azurfa. Saboda haka in ana batun jimlar dukiyoyi ne, ka ga zinare da azurfa ne, su ma din zinare da azurfan, wadanda aka maishe su kudi na kashewa, aka yi masu tambari kenan, Nakash, aka ce masu Dinar da Dirham. Sune ake da kiman dinare 20 ya kai nisabi ko Dirhami 200, cikakken mulki, cikakkiyar shekara, sannan zakka ta hau kansu. Amma shi kudi irin wannan wanda muke yi da takardu, to zakkarsu ba zai zo a babin Dinari da Dirhami ba, sai dai ya zo a babin zakkar ribar dukiyoyi, wanda yake mustahabbi ne yin haka nan. Saboda haka ka ga za ka iya ba da zakka kenan da Naira, amma ba a unwanin Dinari da Dirhami ba, a unwanin ribar ciniki. Saboda haka muna iya cewa a unwanin ribar ciniki, eh zai iya hawa, amma ba a unwanin dinare da azurfa ba. Domin kuskuren da wasu suke yi shi ne sun dauka shi takardar kudin shi ne za a komar da kimarsa a dinare da dirhami a ba da zakka. In haka ne sai mu ce a'a. Ba ina nufin Naira ta arce wa zakka ne kwata-kwata ba, za ta iya shiga a wani babin.

TAMBAYA: Allah shi gafarta Malam, yaya ake zama da matan aure fiye da daya a mazhabin iyalan gidan Manzo?

Daga Muhammad Auwal Pandogari

SHAIKH ZAKZAKY: Wannan yana bukatar ya karanta babi, ko ma littafi sukutum wanda ya shafi wannan. Amsa irin wannan ba za ta wadatar da shi ba. Amma illa iyaka, shi zama din ya shafi abubuwa da dama. Ya shafi kyakkyawar mu'ashara, ya shafi nafaka, ya shafi rabon kwana, ya shafi tufatarwa da wurin kwana da ire-irensu wadanda suke lallai ba zai yiwu in amsa masa a cikin dan gajeren magana ba. Sai dai in ce ya duba Risala amaliyya ta wani Mujtahidi dangane da abin da ya shafi wannan. Da ma littafai da dama wadanda suka shafi sha'anin zaman iyali, wanda yake kuma irin su na da yawan gaske a rubuce-rubucen Malamanmu. Alal misali yana iya duba littafin Ayatullahi Muddahari dangane da Matsayin mata a Musulunci. Da kuma littafin Ayatullah Ibrahim Amini, dangane da zaman iyali. Da kuma wadansu littafai masu dama wadanda suka shafi wannan bangare. Insha Allahu zai sami bayani.

TAMBAYA: Allah shi gafarta Malam, yaya ake neman aure da kuma ka'idodinsa a Musulunci?

Daga Muhammad Ibrahim Potiskum Jihar Yobe

SHAIKH ZAKZAKY: A takaice dai waliyyan mace su suke ba da aurenta, kuma su akan bidI auren a wurinsu, ko da kuwa za mu kaddara cewa ma'aura biyu din - mace da namiji- sun ga juna suna son juna, amma dai za a kai magana ta aure ne wajen waliyyinta a bida. A yayin da aka amsa za a daura masu aure akwai abin da ake ce ma khidba, in aka amsa cewa wance za ta auri wane, to bayan wannan kuma zai zama haramun wani ya zo ya ce shi ma yana son ya aure ta. Sannan kuma sai akadi, wanda yake shi kalmomi ne na siga da suke tabbatar da shi, wanda yake dole ya samu ijabi da kabul, wato "na aurar," "na karba." "Na aurar," a bangaren Waliyyi, "na karba," a bangaren mai aure ko Wakilinsa "Na karba masa," Wane misali. Sai kuma lazim sadaki, sannan akwai i'ilanin aure, walima. Karin bayani yana iya duba littattafan fikihu da suka shafi babin aure.

.
Copyright © 2018~2022.
( Uzairu Badamasi Sufi )
Harkarmusulunci@yahoo.com
All rights reserved

Bamu Da Alhakin Tallar Da Ake Sawa Akan Wannan Website Din


XtGem Forum catalog